Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana ayyana Injiniya Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya ci zaben Gwamnan Kano na zaben Gwammna Jihar Kano da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Da yake bayyana sakamakon zaben, Shugaban Tattara Sakamakon Zaben, Farfesa Ahmad Tukur, wanda malami ne a Jamiar Ahmadu Bello da ke Zariya ya bayyana haka a dakin tattara sakamakon zabe da ke kano