Tinubu ya roki jami’an tsaron dasu taka birki ga Peter Obi akan kalaman tunzuri da yakeyi

Shugaban kasa Mai jiran Gado Ahamad Bola Tunubu ya roki jami,an tsaron kasar nan dasu taka birki ga Peter Obi dan takatar shugaban kasa a Labor Party akan kalaman tunzuri da yakeyi a kasar nan.

Tinubu wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabareru da ya gabata ya kayar da Peter Obi wanda yazamo na uku a zaben,amma daga baya Aka zargi Peter Obi ya fara amfani da wasu kafafen yada
labarai yana kamalan tunzuri ga magoya bayansa .

Haka Kuma Shugaban kasa mai jiran Gado Bola Tunubu ya zargi Peter Obi da amfani da wasu kafafen yada labarai yana kalaman na tunzuri ciki harda ikirarin cewa shine ya lashe zaben shugaban kasa.

Cikin wata takarda da daraktan Kwamatin yakin neman zaben Bola Tinubu Mr Bayo Onanuga ya fitar yace akwai bukatar ita kanta hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta taka birki ga irin
wandanan kafafen yada labarai da suke baiwa Peter Obi dama yana maganganu na soki Buruzu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *