Hukumar yaƙi da cin-hanci da almundahanar kuɗaɗe ta Najeriya ICPC ta ce jami’anta sun kama mutane huɗu bisa zargin sayen ƙuri’a a jihohin Sokoto da Katsina.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta kama mutanen ne ranar Asabar a lokacin da ake gudanar da zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi.
Haka kuma hukumar ta ce an kai wa jami’anta hari tare da raunata mutum guda a jihar Sokoto.
ICPC ta ce an kai wa jami’an nata harin ne a daidai lokacin da ta kama mutum uku masu sayen ƙuri’a a zaɓen da aka gudanar jiya Asabar.