EFCC ta kama kimanin mutane 65 da suka aikata laifukan sayen kuri’a yayin zaben ranar Asabar

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa arzikin Najeriya ta’annati tace ta kama kimanin mutane 65 da suka aikata laifukan sayen kuri’a yayin zaben ranar Asabar 18 ga watan Maris a jihohi 28.

Hukumar ta ce jami’anta a shiyyar Ilorin sun kama mutum ashirin wadanda ake zargi, yayin da wasu 13 kuma aka kama su a jihar Kaduna.

Tawagar hukumar da ke sa ido kan zaben a Port Harcourt sun kama kimanin mutum 12 bisa samun su da aikata laifukan da suka shafi bai wa masu zabe kudi domin jan ra’ayinsu ga dan takarar da suke goyon
baya, yayin da kuma aka cafke mutum hudu a Calabar ta jihar Kuros River.

Sauran wadanda ake zargi an kama su ne a jihohin Gombe da Sokoto da Kebbi da kuma Neja.

Wadanda aka kama a Kaduna sun hada da maza 10 da mata uku a cewar EFCC.

Jami’an hukumar dake tattara bayanan sirri ne suka kama su a lokacin da suke kan aikin sa ido a zaben.

A jihar ta Kadunan dai, tawagar EFCC karkashin ACE II Esmond Garba ta kama wani mai suna Buhari Muhammad a rumfar zabe ta 002 a Dogara Yaro Dagari.

An kama shi da wasu takardu wadanda ya tabbatar cewa zai yi amfani da su ne wajen gano mutanen da suka zabi jam’iyyarsa.

Tawagar ta hukumar ta EFCC a yankin Kabala Doki da ke Kaduna ta kama mutum biyu da ake zarginsu da sayen kuri’u.

An kuma same su da kudi kimanin N67,500 da jerin sunayen masu zabe da lambobin katin zabensu da kuma bayanan asusunsu na banki.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa wadanda ake zargin suna bayar da kudi ko su aika kudi ta intanet ko tura katin waya ga masu zabe domin sauya musu ra’ayi su zabi dan takararsu.

Binciken da aka yi a wayoyinsu ya nuna akasarinsu sun tura kudi zuwa asusun wasu masu zabe da ke jerin sunayen da aka gano a hannunsu.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka gano daga wajen wadanda ake zargin akwai katunan zabe da kudi da jerin sunayen mutanen da asusun bankinsu da kuma katin waya.

Wasu jami’an na EFCC sun kuma cafke mutum biyu a jihar Neja saboda zargin sayen kuri’a.

A birnin Fatakwal babban birnin jihar Rivers , jami’an EFCC sun kama
mutum 10 da suma ake zarginsu da sayen kuri’u.
An kuma kama wata shugabar mata Esther Asuquo a Kuros River tare
da wasu mutum biyu bisa zarginsu da sayen kuri’u.
A Gombe, tawagar ta EFCC karkashin Faruk Dogondaji ta kama mutum
10 bisa zarginsu da sayen kuri’u sun kuma gano atampopi 43 da kudi
sama da miliyan daya.
Ana ci gaba da gudanar da bincike a kan mutanen da ake zargi, kamar
yadda EFCC ta bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *