Jam’iyyun APC da NNPP a jihar Kano sun umarci magoya bayansu da su ɗunguma cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe domin kaucewa maguɗi tare da kare abinda kowa ya zaba.
Da farko Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba shine ya fara bada umarnin a madadin APC yayinda jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya umarci nasa
magoya bayan a madadin NNPP.
A sanarwar da ya fitar, Muhammadu Garba ya ce kiran ya zama wajibi saboda kare ƙuri’un da suka kaɗa.
Shi ma Kwankwaso ya saki wani gajeren bidiyo ne inda ya ce sakamakon akwatunan da aka bayyana ya ba NNPP ƙwarin gwiwar
samun nasara a zaɓen.
Don haka ya umarce magoya baya su bai wa ƙuri’unsu kariya a
matakan mazaɓu, da ƙananan hukumomi, da kuma jiha.
Rahotanni nacewa an kammala zaɓen a rumfunan zaɓen dake faɗin
jihar Kano, tun a yammacin jiya in da kuma aka shiga tattara sakamako.
Duk dacewa akwai jam’iyyu da yawa da suka shiga takarar kujerar
gwamnan jihar Kano, amma ƴar manuniya ta nuna cewa tsakanin
Nasiru Yusuf Gawuna na APC da Abba Kabir Yusuf na NNPP ake sa
ran samun wanda zai yi nasara.