Matasa sun hana zabe a jihar sakkwato

Wasu gungun matasa sun hana ruwa gudu yayin da ake shirin soma zaben gwamna da na ’yan majalisar dokoki a Jihar Sakkwato.

Rahma ta ruwaito cewa, ma’aikatan zabe sun kwashe kayansu a rumfar zabe mai lamba 027 ta Aliyu Kyari kan hatsaniyar da matasa suka tayar suna masu cewar ba su yarda da a yi zaben ba.

Tun da sanyin safiyar wannan Asabar din dai matasa maza da mata suka fara shiga layi yayin da ma’aikatan zaben suka hallara, sai dai kuma gudanar da zaben ya gagara a rumfar inda a karshe aka kwashe kayan zabe.

Daya daga cikin ma’aikatan zaben, Ibrahim Yakubu, ya ce babu tsaro a rumfar don haka ba za su yi zabe ba ganin yadda matasa suke ta rigima a rumfar.

A cewar Yakubu, “dole mu dakatar da zaben duk ba mu fara ba saboda babu yadda za a yi mu fara aiki ana hatsaniya.”

Muhammad Bashar, wani matashi mai shekara 25 ya ce “haka kawai wasu matasa suka zo suka tayar da rigimar cewa ba za a yi zabe ba.

“Yanzu burinsu ya cika don gashi an watse.”

Matashin ya ce rumfar tana da masu jefa kuri’a 500, “amma yanzu an yi hasarar kuri’unsu daga wasu marasa kishin kasa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *