Gobara Ta Tashi A Kasuwar Biu

Gobara ta tashi a Babbar Kasuwar Biu da ke Jihar Borno ana tsaka da zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jiha.

Mataimakin Shugaban Tsaro ta Sa- Kai ta CJTF, Aliyu Isa ya ce, sun samu sanarwar tashin gobarar ce da misalin karfe 9 na safiyar ranar Asabar.

Ya shaida mana cewa gobarar ta yi barna sosai a bangaren masu sayar da katako a kasuwar, amma jama’ar gari sun yi taron dangi wajen shawo kanta.

Amma ya cewa duk da haka, gobarar “Ta kawo tsaiko ga harkokin zabe a sassan garin, ko da yake daga baya jama’a sun koma sun ci gaba da zabe.”

Mako uku ke nan bayan tashin wata gobara da ta lakume shaguna sama da 10,000 a Babbar Kasuwar Monday da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

An yi gobarar Kasuwar Monday ne washegarin zaben shugaban kasa da ’yan majalisar dokoki ta tarayya da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu.

A baya-bayan nan ana yawan samun gobara a kasuwanni.

Ko a cikin makon nan, an samu gobara a Kasuwar Singa da ke Kano, inda aka tafka asarar miliyoyin Naira.

Gobarar Kasuwar Singa ita ce ta hudu cikin dan lokaci a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *