An Kama Matashi Da Makamai A Kano

Jami’an tsaro sun cafke wani matashi da muggan makamai a Unguwar Chiranchi da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Jami’an tsaron sun cika hannu da matashin yayin da aka soma ruguntsumi a unguwar ana tsakar soma gudanar da zaben gwamna da ’yan majalisar dokoki na jiha.

A maimakon a fara zabe kamar yadda aka tanada, rikici ya mamaye wani yanki na Unguwar Chiranchi da ke zaman mazabar dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida da kuma Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas.

Cikin wani hoton bidiyo da wakilinmu ya nada, jami’an ’yan sanda rike da bindigogi ke ta kai kawo a tsakanin jama’a da ke nuna alamar tsugune ba ta kare ba.

Unguwar Chiranci wadda ke cikin Karamar Hukumar Gwale, tana da tarin rumfunan zabe, inda kuma tun ba yanzu ba an yi hasashen babu lallai a kwashe lafiya saboda tsananin adawa ta siyasa da ke tsakanin jam’iyyar NNPP da kuma APC mai mulki a jihar.

Tuni jami’an ’yan sanda da ke zaman jiran ko ta kwana suka bukaci karin jami’ai yayin da wakilinmu ya hangi wasu matasa suna musayar kutufo a tsakaninsu.

Bayanai dai sun ce ’yar tazara kalilan ce tsakanin rumfunan zabe da jiga-jiga jam’iyyun mabambanta za su kada kuri’arsu.

Sai dai duk da wannan ruguntsumi, an kammala shirin soma aiki zabe a mazabar da ke Sakandaren GSS Balarabe Haladu a Unguwar ta Chiranci, inda ake sa ran nan da zuwa wani lokaci Abba Gida-Gida zai fito ya kada kuri’arsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *