EFCC ta damke wani Farfesa bisa zargin damfarar N1.4bn
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da Farfesa Uche Chigozie Edwin a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Legas, bisa zargin damfarar N1.4bn.
An gurfanar da Edwin tare da wasu kamfanoninsa biyu.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da hukumar ta fitar ta shafin Twitter a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, Edwin ya gurfana a gaban kotu kan tuhume-tuhume 11 da suka hada da hada da musayar kudade.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Hukumar EFCC ta shiyyar Legas, a ranar 16 ga Maris, 2023, ta gurfanar da wani Farfesa Uche Chigozie Edwin a gaban kotu bisa zarginsa da damfarar N1.4bn a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo na babban kotun tarayya da ke zaune a Ikoyi, Legas.
“An gurfanar da Edwin ne tare da kamfanonin sa, Visionary Integrated Consulting Limited, NEMAD Associates Limited da Revamp Global Enterprise akan tuhume-tuhume 11 da suka hada da hada da karkatar da kudade da suka kai N1,473,367,046.04.
Atiku Abubakar ya caccaki kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan “neman amincewa” bayan zaben ranar 25 ga watan Fabrairu a Najeriya.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya zargi jam’iyyar APC da rokon shugaban kasar Amurka Joe Biden ya taya Bola Tinubu murna.