EFCC ta gurfanar da wani ɗan ƙasar Indiya saboda zargin satar kuɗi.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da wani ɗan ƙasar Indiya mai suna Chandra Prakash Singh, a gaban wata kotu da ke jihar Legas saboda zargin satar kuɗi da ya kai dala 200,000.

Hukumar ta ce a ranar 16 ga watan Disamban 2020 wanda ta ke zargin ya cire kuɗi $90,000 daga wasu
asussa na bankin da ba mallakinsa ba wanda kuma ya saɓawa doka.

Sai dai wanda ake zargi ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.

A don haka ne, lauya mai gabatar da ƙara B.B Bala ya bukaci da a ci gaba da tsare shi, har sai an sake saka
ranar ci gaba da sauraron shari’ar.

Sai dai lauya mai kare wanda ake ƙara, Efe Solomon Izokor, ya roki kotu da ta ba da belin wanda ake zargi.
Amma Barrister Bala ya bukaci lauyan da ya rubuta bukatar neman belin sannan ya kawo ta gaban kotun
domin ba ta damar amsawa yadda ya kamata.

Mai shari’a Oweibo ya ɗage zaman sauraron karar zuwa 27 ga watan Yunin 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *