Hukumar gudanarwar kwalejin fasaha ta jihar Kogi, Lokoja, ta kori wasu manyan malamai hudu daga aiki bisa zarginsu da aikata muggan laifuka da suka hada da zamba, cin zarafi da sauran laifuka,kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Jami’ar hulda da jama’a ta cibiyar, Uredo Omale ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Lokoja ranar Juma’a.
Ta ce an kori malaman da abin ya shafa ne saboda rashin da’a, wanda ta danganta da “cin zarafin ta hanyar jima’i, cin zarafin dalibai mata, gujewa aiki, rashin biyayya, karya bayanai, rashin biyayya ga doka da karkatar da tallafin horarwa na TETFUND”.
A cewarta, korar malaman ya biyo bayan amincewar majalisar gudanarwar kwalejin fasaha ta jihar Kogi a taronta na 68.
“Malaman da aka kora kan laifuffukan a akwai (Mr. Ipinmoroti Samuel Adejoro da Misis Adegoke Kehinde Vivian), sun hada da rashin bin doka da oda, karya takardar shaidar samun tallafin horo da karkatar da tallafin horon da aka ce ya kai N22,676,500.00 da N21,000004 ” sanarwar ta jaddada.
Kwamitin binciken ya kuma umurci mahukuntan cibiyar da su yi amfani da hanyoyin da suka dace wajen kwatowa daga hannun Mista Ipinmoroti da Uwargida Adegoke jimillar kudaden da suka kai N22,676,500 da kuma N21,204,000, kasancewar kudaden da ake zargin sun karba a matsayin tallafin horaswa ba tare da sun yi horon ba a jami’ar da aka amince da ita a Malaysia.
Har ila yau, sanarwar ta kara da cewa “An kori Mrs Slyvester Ojone Blessing daga aiki daga ranar 5 ga watan Janairu, 2020 zuwa 31 ga watan Yuli, 2022 kuma ya mayar da kudaden da ya kai N1,356,653.79, kasancewar albashin da gwamnati ta karbo ba a samu ba a tsawon lokacin da ta gudu”.
A wani labarin kuma, majalisar gudanarwar kwalejin ta amince da karin girma ga wasu malamai takwas zuwa manyan malamai.
Sai dai shugaban majalisar gudanarwar ya yabawa mahukuntan cibiyar a karkashin jagorancin Dokta Salisu Ogbo Usman, bisa jajircewar da suka yi wajen yin hidima, inda ya yi kira da a kara yin garambawul ga ci gaban ilimi mai dorewa a cibiyar.
A halin da ake ciki, shugaban kwalejin na cibiyar, Dr Usman ya yaba wa shugaban da membobin majalisar gudanarwa bisa dorewar goyon baya da kwarin gwiwa.
Shugaban ya yabawa gwamna Yahaya Bello bisa yadda ya bada damar gudanar da gyare-gyare ta hanyar rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na kwalejin.
Yayin da za a gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a gobe Asabar, wasu mazauna jihar Ribas sun shiga tsakani kan wadanda za su kada kuri’a, musamman na kujerar Gwamna.
Wasu masu lura da al’amura dai na ganin cewa akwai yiyuwar samun nasara a zaben gwamna da ‘yan takarar majalisar jiha na jam’iyyar PDP.