’Yan kasuwa sun bayyana cewa ba za su fara karbar tsoffin takardun har sai Buhari ya bada umarni.

’Yan kasuwa a wasu yankunan kasar nan sun bayyana cewa ba za su fara karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 ba har sai sun ji Shugaban Kasa Muhamamdu da bakinsa ya ce su fara karba.

Yan kasuwa da kwastomominsu jihohin Kaduna da Legas da kananan hukumomin Abaji da Kwali a Yakin Babban Birnin Tarayya na kin karbar tsoffin kudin ne, a washgarin da bankunan kasuwanci suka fara bayar da su, bisa umarnin Babban Bankin Najeriya (CBN).

Sai dai a Jihar Kano, harkokin kasuwanci sun fara komawa yadda aka saba, tun bayan da bankuna suka fara bayar da tsoffin kudi, kuma mutane suka ci gaba da amfani da su a harkokin kasuwanci.

Haka kuma an samu raguwa mutane da ke neman cirar kudi, dai dai wasu bankunan sun bayyana cewa tsabar kudin da ke hannunsu ya kare, shi ya sa ba a ganin layin mutane a ATM dinsu domin cirar kudi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *