NBC ta ci tarar kafofin yaɗa labarai 25

Hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta kasa NBC, ta ci tarar kafofin yaɗa labarai 25 saboda saba ƙa’idar aiki da dokar zaɓe a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki na tarayya da aka yi a watan da ya wuce.

Haka kuma hukumar ta NBC ta yi wa wasu gidajen rediyo 16 gargaɗi na ƙarshe kan laifukan da suka danganci zaɓe.
Gidan rediyo 17 ne hukumar ta zarge su da yaɗa abubuwan na siyasa, yayin da ya rage sa’a 24 a yi zaɓe, wanda hakan ya keta doka.

Uku daga cikin gidajen rediyon sun fuskanci tuhumar sanya abubuwa na neman haddasa rikici, yayin da hukumar ta tuhumi hudu daga cikinsa da laifin neman raba kai na kabilanci da addini.

An ci tarar tasha ɗaya bisa laifin bayyana sakamakon zaɓe tun kafin hukumar zaɓe ta sanar.

A wata sanarwa shugaban hukumar ta NBC, Balarabe Shehu Illela, ya buƙaci gidajen talabijin da rediyo da su tabbatar da sun kiyaye da dokokin aikinsu da kuma na zaɓe kafin zaɓen da za a yi ranar Asabar na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a Najeriyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *