Haramtacciyar ƙungiyar ƴan a-ware ta Biafra, (IPOB) da ke kudancin Najeriya ta zama ta goma a cikin ƙungiyoyin da suka fi aikata ta’addanci a duniya.
Wata ƙididdiga da rahoto (Global Terrorism Index (GTI) na wannan shekara ta 2023 da aka fitar na duniya game da ta’addanci wanda ya sanya ƙungiyar a wannan mataki, ya ce hare-hare 40 da kisan gilla 57 da ta aikata a 2022 su suka sa ta kai wannan mataki.
Daga cikin kisan gillar da IPOB din ta aikata akwai na hallaka wasu sojojin Najeriya ango da amarya, wadanda ta gille musu kai, da kisan ‘yan arewacin kasar da ke kudu maso gabashi da kuma kisan jami’an tsaro da dama.
Rahoton wanda ya bayyana ƙungiyar ta IPOB da cewa mai haɗarin gaske ce a ta’addanci, ya sanya Al-Shabaab a matsayin ta ɗaya a duniya wajen ta’addanci.
Ƙungiyar ta Al-Shabaab wadda take da ƙarfi a gabashin Afirka rahoton ya nuna cewa ta yi kisan gilla 784 da hare-hare 315, yayin da ƙungiyar IS ta lardin Khorasan (ISK) ta yi kisa 498 da kuma hare-hare 141.
Sai kuma ƙungiyar Jamaat Nusrat Al-Islam wal Muslimeen (JNIM), wadda ta
hallaka rayuka 279 da kai hari 77, yayin da Balochistan Liberation Army
(BLA), ta hallaka rai 233 ta kai hari 30.
Ita kuwa ƙungiyar IS ta yammacin Afirka (ISWAP), ta kasance ta 6 a rahoton
inda ta hallaka rai 219 da kai hari 65, yayin da Boko Haram ke bi mata baya
da kisan kai 204 da hare-hare 64.