An samu nasara wajen yaki da ta’addanci kasar nan idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata

Rahotanni na nuni da cewar an samu nasara wajen yaki da ta’addanci kasar nan idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata inda kasar ce ke a mataki na 8 sabanin na 6 da ta ke a shekarar 2021.

A cewar rahoton bincike da ake yi gameda ayyukan ta’addanci da aka fitar a wannan shekarar, ya nuna cewar ayyukan ta’addanci a karon farko sun ragu sosai a kasar tun bayan shekarar 2011.

Daga tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020, Najeriya na mataki na hudu a jerin kasashen da aka fi samun ta’addanci a duniya, duk da cewa lamarin ya fi kamari a shekarar 2016 da 2015 da kasar ke a mataki na 2.

Kungiyoyin masu ta da kayar baya irin su Boko Haram da kuma ISWAP sun yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a shiyar Arewa maso Gabashin kasar, a hare-haren da suke kaiwa.

A cewar rahoton, a shekarar 2021 mutane 497 suka mutu sanadiyar ayyukan ta’addanci inda kuma adadin ya ragu zuwa 385 a shekarar da ta gabata.

Haka nan kuma, adadin hare-haren ta’addancin da aka kai a shakarar 2021 ya ragu zuwa 214 sannan a shekarar da ta gabata ya kara yin kasa zuwa 120, wanda shine karo na farko da aka samu irin wannan raguwa tun shekarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *