Karancin man fetur na ci gaba da ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya

A yayin da ake gab da gudanar da zaben gwamnoni da na M‘yan majalisun jihohi a Najeriya, karancin man fetur na ci gaba da ci wa ‘yan kasar tuwo a kwarya, da hakan zai iya zama matsala wajen yin tafiye-tafiye zuwa jihohi don gudanar da zaben.

Za a iya cewa a Najeriyar tun tsakiyar damunar bara a ke ganin man fetur din na tashin gauron zabi da karanci a kasuwannin kasar.

A yanzu a na ganin kasashen da suka ci gaba wajen kafuwar tattalin arziki da kimiyya sun fara ajiye man fetur a matsayin wani babban jigo da ke tallafawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasa.

Har yanzu a Najeriya kasar ta dogara ne da man fetur duk da cewa kasa ce da ke da dimbin arzikin ma’adanai da kasar noma.

Mutane kan shafe sa’o’i a kan layi a gidajen mai wanda hakan ke kawo matsala ko cikas a sana’o’i har ma da lamuran su na yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *