INEC: “Bamu da wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara da muke mara wa baya a kasarnan”.

Hukumar zabe ta kasa INEC tace ba ta da wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara da ta ke mara wa baya a
kasarnan.

Kwamishinan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta KasaINEC, Maj-Gen. Modibo Alkali ya ce hukumar ba ta da wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara da ta ke mara wa baya a kasar.

Alkali ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki da aka yi da wakilan dukkanin jam’iyyun siyasa a Talatar nan a jihar Sakkwato.

Ya ce hukumar zaben ba za ta lamunci maimaita kura- kurai da aka samu a zaben shugaban kasa da na ƴan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *