“Mun gyara dukkan matsalolin da ta fuskanta a yayin zaben da ya gabata gabanin zaben Gwamnoni” – INEC

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta gyara dukkan matsalolin da ta fuskanta a yayin zaben Shugaban Kasa da na ’Yan Majalisun Tarayya gabanin zaben Gwamnonin da za a yi a karshen makon nan.

Kwamishinan Hukumar mai kula da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan yayin
tattaunawarsa da manema labarai.

Ya ce INEC ta koyi muhimman darussa, kuma za ta yi amfani da su wajen gyara matsalolin da za a iya fuskanta a zaben na Gwamnoni.

Festus ya kuma ce sun yi iya bakin kokarinsu wajenMtabbatar da an magance matsalar sashen duba
sakamakon zabe na shafin hukumar, wanda aka fi sani da IReV.

Ya ce yanzu haka sashen yada labaran hukumar ya yi shirin ko ta kwana, ko da za a fuskanci kalubale yayin dora sakamakon zabe daga rumfunan zabe a shafin.

Ko a makon da ya gabata, sai da Kotun Daukaka Kara ta amince wa hukumar INEC da ta sake sabunta bayanan da ke kan na’urar tantance masu zabe ta BVAS gabanin zaben na karshen mako.

Sai dai daga bisani INEC ta sanar da dage zaben zuwa ranar 18 ga watan Maris, a maimakon 11 ga wata don samun damar sabunta bayanan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *