“Gobarar da ta tashi a kasuwar Singa ta samo asali ne daga ɗakin sanyaya ruwa”. – Hukumar kashe gobara ta jihar Kano

Rahotanni na nuni da cewa gobarar da ta tashi a kasuwar Singer ta haifar da asara mai ɗinbin yawa.
Rahotanni sun ce wutar ta ƙona dukiya wadda har yanzu ba a iya tantancewa ba.

Wannan dai shi ne karo na hudu da ake samun gobara a baya-bayan nan a kasuwanni daban-daban na jihar Kano.

Bayanai na cewa gobarar ta auku ne da tsakar dare sanadiyar fashewar wani babban abin sanyaya ruwa a
layin Savannah cikin babbar kasuwar ta Singer.

Wani mutum da lamarin ya auku a kan idonsa ya ce wutar ta yi mummunar barna.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da aukuwar gobarar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya ce wutar ta samo asali ne daga ɗakin sanyaya ruwa, sannan ya yaɗu zuwa wasu kantunan.

Ya ƙara da cewa rashin kyakkyawan tsarin ajiye kaya a kasuwar ya taimaka wajen iza wutar.

Sai dai ya ce ba a samu rahoton rasa rai ko kuma na jikkatar wani ba a sanadiyyar gobarar.

Wannan dai ita ce gobara ta uku cikin kasa da wata biyu da ta auku a kasuwanni daban-daban a jihar Kano.

Kasuwar Singer dai babbar kasuwa ce da ake hada-hadar kayan masarufi daga sassan Najeriya har ma da ketare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *