CBN ya magantu kan halin da ake ciki game da tsoffin Naira bayan hukuncin kotu.

Babban Bankin Najeriua CBN umarci bankuna su ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi na N200, N500, N1,000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Mukaddashin Daraktan Sadarwa na Babban Bankin, Isa AbdulMumin ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Hakan dai na zuwa ne kwanaki 10 bayan da kotun kolin kasar ta yanke hukuncin cewa a cigaba da amfani tsohon takardun kudin Naira tare da sabbin har zuwa karshen shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *