Kungiyar tuntuba ta arewa (ACF) ta yi gargadin cewa ci gaba da kin bin umurnin kotun koli dangane da amfani da tsoffin kudi na iya haddasa rikici a kasar nan.
A wata sanarwa da ya saki, babban sakataren kungiyar ta ACF, Murtala Aliyu, ya yarda da matakin gwamnonin jiha wadanda suka maka gwamnatin tarayya a kotu kan manufar.
Ya ce yanayin yadda babban bankin Najeriya (CBN) ke tafiyar da lamura a yanzu ya haifar da damuwa game da yancin yan Najeriya kasancewar ya shafi yancinsu na samun kudaden shiga ta hanyar da suke so.
Ya kuma koka kan dandazon jama’a da dogon layukan da ake yi a bankuna da akwatunan ATM a fadin kasar yayin da mutane ke fafutukar samun sabbin kudi wanda har yanzu basu wadata ba, lamarin da ya haifar da zanga- zanga da sauransu.