El Rufai ya rantse cewa bai taba satar kuda koda naira daya ba daga lalitar jihar

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufai ya rantse da ubangijinsa Allah Sunahanahu Watala cewa bai taba satar kuda naira daya na kudin jama,ar jihar Kaduna tsawon shekaru 8 da ya shafe yana mulkin jihar.

Anjiyo gwamna Nasiru Elrufai ne na wannan ikirari a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na zamani.

Gwamnan na ya kuma kalubalanci duk wani dan Kaduna da yake jin cewa ya saci kudin jihar koda naira daya ne ya kawo hujjarsa.

Sannan yace babu wani gida da ya sanya a Dubai ko klasashen waje ko cikin Najeriya in banda gidan da yake ciki a yanzu.

Gwamna Elrufa na wannan bugun Kirjin ne El-Rufai lokacin da yake zayyana yadda gwamnatin sa tayi ayyuka masu nagarta ba tare da rage kuɗi ko yin ɗingushe ba a cikin kuɗin kwangilolin da ake bayar wa a
lokacin mulkin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *