Akalla gawarwakin mutane 10 ne aka gano bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai hari Unguwar Wakili a karamar hukumar Zango Kataf ta jihar Kaduna.
A Wata sanarwa da mataimaki na musamman a kafafen yada labarai na shugaban karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar, Yabo Chris Ephraim, ya raba wa manema labarai, ya ce,a dalilin kai wannan hari an sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Ungwan Juju, Mabuhu, Ungwan Wakili da Zango.
Sanarwar ta kara da cewa kafa dokar ta-bacin na daga cikin matakan da za a dauka na dakile matsalolin da suka shafi sha’anin tsaro a yankin da kuma baiwa sojojin Nijeriya damar dawo da zaman lafiya a
yankin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, bai ce uffan ba har zuwa lokacin hada wannan rahotonv 1.