Sani Yakasai Ya Rasu

Fitaccen dan kasuwa kuma dan kwangila a Jihar Kano, Alhaji Sani Dahiru Yakasai ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin dai shi ne shugaban kamfanin gine-gine na SDY, wanda yana daya daga cikin jiga-jigan kamfanonin kwangila a jihar da kewaye.

A cewar wata majiya, Alhaji Yakasai ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Majiyar ta kara da cewa, Yakasai ya rasu yana da shekaru 68 a duniya kuma ya bar matansa da ’ya’yansa da jikoki.

An yi jana’izar sa a Kofar Kudu ta Fadar Sarkin Kano da misalin karfe 8 na safiyar wannan Juma’ar, sannan an binne gawarsa a makabartar Tarauni.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje; Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero da Sanata Ibrahim Shekarau, na daga cikin dimbin musulmin da suka halarci jana’izar dan kasuwan wadda ya rasu a jiya Alham

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *