MDCN ta shawarci sabbin likitoci da aka horas da su a kasashen waje da su yi la’akari da yin aiki a Najeriya

Majalisar likitoci masana kiwon lafiyar hakori ta Najeriya ta shawarci sabbin likitocin da aka horas da su a kasashen waje da su yi la’akari da yin aiki a kasar nan, maimakon fita kasashen waje domin yin aikin.

Majalisar ta MDCN ta ce da yawa daga cikin likitocin da suka yi hijira zuwa wasu kasashe, a halin yanzu suna nadamar abin da suka aikata, saboda suna fuskantar wariya.

Magatakardar majalisar Dokta Tajudeen Sanusi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin bikin kaddamar da dalibai 469 da suka kammala karatun likitanci da kuma wadanda suka kammala
karatun likitan hakora guda takwas.

Sanusi ya kuma gargadi sabbin likitocin da aka horas da su guji shiga yajin aikin kungiyoyin likitoci.

Ya ce duk da cewa likitocin na da ‘yancin walwala da tsarin mulki ya ba su, amma ba a dauke su a matsayin mambobin kungiyar likitoci ta NARD ba.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, wanda ya samu wakilcin daraktar tsare-tsare, bincike da kididdiga ta ma’aikatar, Dr Ngozi Azodo, ya koka da yadda likitocin ke gudun hijira, sannan ya bukaci likitocin da aka horas da su yi wa majinyata hidima ba tare da son rai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *