Kotu ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bar wasu masu katin zabe na wucin gadi su kada kuri’a a zaben gwamnoni da majalisun dokokin jiha da ke tafe ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ba da umarnin ne bayan wasu ’yan Najeriya biyu sun shigar da karar neman INEC ta bari masu katin zabe na wucin-gadi su yi zaben da ke tafe.
Sai dai ya bayyana cewa izinin amfani da katin zabe na wucin-gadi bai shafi sauran masu zabe ba, kasancewar masu karar ba su shigar da karar a matsayin na wakilci ba.
Amma ya bayyana cewa babu inda kundin tsarin mulkin Najeriyana 1999 ko Dokar Zabe suka ce masu katin zabe na dindindin kadai ne za su kada kuri’a.
Ya ce hatta sashe na 47 na dokar zabe, katin zabe kawai ya yi magana, bai ce sai na dindindin ba.
Da yake magana kan hukuncin, lauyan masu kara, Victor Opatola, ya bayyana hukuncin kotun a matsayin nasara ga ’yan Najeriya da suka sha wahalar yin rajisar zabe, amma ba su samu katinsu na dindindin saboda kurewar lokacin, kuma ba laifinsu ba ne.
A cewarsa tun da har wadanda yake wakilta sun yi duk abin da doka ta ce na yin rajista, amma har lokacin ba da katin dindindin ya wuce ba su samu nasu ba, to ya kamata a bari su yi zabe. Opatola, ya ce abin da ya kamata bisa adalci, shi ne a bar sauran.
’yan Najeriya suka cika sharudda kamar wadanda yake wakilta
suka cika, su yi zabe, domin bayanan da ke katin zabe na wucin-
gadi su ne ke kan katin dindindin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a
halin da ake ciki, wajibi ne bin umarnin kotun ga INEC, har sai
idan kotun daukaka kara ta jingine hukuncin.
Tuni dai a nata bangaren hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa
INEC ta sha alwashin kalubalantar wannan hukunci a gaban kotun
daukaka kara.