Buhari ya jajanta kan hatsarin da ya rutsa da motar ma’aikatan BRT na jihar Legas

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta kan hatsarin da ya rutsa da motar ma’aikatan BRT na jihar Legas da kuma jirgin kasa a unguwar Shogunle da ke Ikeja.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Buhari kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Alhamis, shugaban ya ce hatsarin na da ban tausayi da kuma bakin ciki matuka.

Buhari ya kuma yabawa hukumomin jihar Legas da hukumomin gwamnatin tarayya bisa gaggauta fara gudanar da ayyukan agaji.

Idan ba a manta ba a safiyar Alhamis ne wata motar bas BRT ta Legas da jirgin kasa dauke da ma’aikata zuwa wuraren aikinsu a Legas suka yi karo da juna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan shida tare da jikkata wasu da dama.

Tuni dai Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku ga wadanda hadarin ya rutsa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *