Yau Duniya ke bikin ranar Mata cike da fatan samar da daidaiton jinsi

Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara ne duniya ke bikin ranar Mata, bikin da ya samo asali tun daga shekarar 1908 lokacin da kungiyar kwadago ta kasa da kasa ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wannan rana a sahun ranakun da ake tunawa da su shekara-shekara a wani yunkuri na samar da hanyoyin magance matsalolin da suka dabaibaye mata a bangarori daban-daban.

An faro bikin wannan rana ne a shekarar 1911, shekaru 3 bayan zanga-zangar mata fiye da dubu 15 a 1908 gangamin da ya nemi ragewa matan wahalhalun da suke yi ciki har da bukatar rage musu yawan lokutan aiki da inganta albashinsu baya ga basu damar kada kuri’a.

Amurka ta fara ayyana ranar a shekarar 1909, karkashin jam’iyyar ‘yan mazan jiya ta Socialist yayinda aka faro bukukuwan ranar a kasashen Austria da Jamus da kuma Switzerland shekaru biyu bayan matakin na Amurka.

A shekarar 1975 ne aka tabbatar da bikin ranar a hukumance inda Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci bikin, kuma taken farko na irin wannan rana a 1996 shi ne “tuna baya da tsara rayuwa ta gaba”.

Bisa al’ada ranar Mata ta Duniya kan zamo dandalin tattauna halin da mata ke cikin a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma rayuwar yau da kullum kama daga ‘yancinsu a fannonin rayuwa, yayinda a irin wannan lokaci ake shirya mabanbantan gangami don fadakarwa dama yaki da nunawa matan wariya

A kasashe da dama kowacce 8 ga watan Maris na kasancewa ranar hutu, ciki har da Rasha wadda bisa al’ada kan kara yawan furannin da aka saba sayarwa akalla kwanaki 3 zuwa 4 kafin ranar.

Taken bikin Ranar Mata ta Duniya a bana shi ne  #EmbraceEquity‘ 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *