INEC ta fitar da jadawalin zaɓaɓɓun sanatocin da suka yi nasara a zaɓen Fabrairun 25

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da jadawalin zaɓaɓɓun sanatocin da suka yi nasara a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Cikin jadawalin da Inec ta fitar, an tabbatar da zaɓukan da aka yi na mazaɓu 109, guda bakwai kuma za a sake yin su yayin da kujera ɗaya kuma take ba kowa a kai saboda mutuwar ɗaya daga cikin masu takara.

A jerin sunayen, Jam’iyyar APC ta lashe mafi yawan kujeru da 55, sai PDP da take da kujeru 33, Jam’iyyar LP kuma ta samu kujeru 7.

Shugaban Inec, Mahmood Yakubu a jawabin da ya yi na baya-bayan nan a ganawarsa da kwamishinonin hukumar zaɓe a Abuja, babban birnin tarayyar kasarnan, ya ce jam’iyyu takwas ne suka samar da sanatoci a zaɓen da ya gabata.

Jam’iyyun sune APC, PDP, APGA, SDP, Labour, NNPP, ADC da YPP.

A cewar Inec, za a sake gudanar da zaɓe a mazaɓun da ba a sanar da wanda ya yi nasara ba bayan zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokoki a jihohi da za a yi ranar 11 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

A cewar Inec, za a sake gudanar da zaɓe a mazaɓun da ba
a sanar da wanda ya yi nasara ba bayan zaɓen gwamnoni
da na ƴan majalisar dokoki a jihohi da za a yi ranar 11 ga
watan Maris ɗin da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *