PDP na gudanar da wata zanga-zanga a shalkwatar INEC Abuja.

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya na gudanar da wata zanga-zanga a shalkwatar hukumar zaɓe ta ƙasa INEC a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban jam’iyyar na ƙasar Iyorchia Ayu, da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen da aka gudanar gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta na daga cikin mutanen da za su jagoranci zanga-zangar.

A wata sanarwar da Ibrahim Bashir ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar ya fitar a madadin daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, ya ce daga cikin mutanen da aka gayyata zuwa zanga-zangar sun haɗar da shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar wato gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel, da daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar wanda shi ne gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

“Gwamnonin jihohin Bayelsa da Edo da Adamawa da Bauchi da Taraba da kuma Osun, sauran su ne tsoffin shugabannin majalisar dattawan ƙasar Sanata David Mark da Sanata Abubakar Bukola Saraki, da kwamitin amintattun jam’iyyar da ‘yan majalisar dattawa da na wakilai na jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki na
jam’iyyar”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar ta kuma umarci jami’an da su sanya baƙin tufafi domin nuna ɓacin ransu a zanga-zangar da za su gudanar a Maitama da ke Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *