Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce’yan siyasa masu rike da madafun iko za a dora wa laifin gazawar Najeriya wajen samun wadataccen abinci.
Ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a wajen wata lacca da aka shirya domin bikin cikarsa shekara 86 a garin Abeokuta a Jihar Ogun.
Obasanjo, ya bayyana damuwarsa kan yadda Najeriya da Afirka suka kasa cin gajiyar ci gaban kimiyya da fasaha domin bunkasa fannin noma.
Ya roki ‘yan Najeriya da su zargi shugabannin kasar nan da rashin kishin wajen mayar da Najeriya jigon samar da abinci a Afirka.
A nasa jawabin, Darakta–Janar na Cibiyar Noma ta Kasa da Kasa (IITA), Dokta Nteranya Sanginga ya koka da cewa, kasashen Afirka duk da an albarkace su da su kasa mai albarka har yanzu tana kashe biliyoyin daloli wajen shigo da abinci.