Sabon zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya shirya tsaf domin tunkarar duk wani sammaci da dan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai yi masa.
A wani taron manema labarai a ranar Alhamis, Atiku ya ce zaben na ranar Asabar da ta gabata wanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta sanar cewa Tinubu ya lashe, a matsayin zabe mara inganci.
Sai dai a wani martani da ya mayar da Festus Keyamo (SAN) ya fitar, Tinubu ya ce, “Shirin Atiku Abubakar na kalubalantar sakamakon zaben abin farin ciki ne.
Atiku dai kamar abokin hamayyarsa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya ce ya shirya zuwa kotu don kalubalantar nasara Tinubu a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.