Kotun Koli Ta Tsawaita Lokacin Amfani Da Tsoffin Kudi

Kotun Koli ta ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira da aka sauya wa fasali har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Kotun kolin ta kuma soke manufofin gwamnatin tarayya na sake fasalin Naira, inda ta bayyana hakan a matsayin saba wa kundin tsarin mulkin kasar na 1999.

Mai shari’a Emmanuel Agim, wanda ya karanta hukuncin da aka yanke, ya ce an yi watsi da korafin farko da wadanda ake kara (Atoni Janar na Tarayya, Bayelsa da Edo) suka yi ne saboda kotu na da hurumin sauraren karar.

Kotun da ta ambaci sashe na 23 (2) na kundin tsarin mulkin kasar, ta ce dole ne rigimar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da Jihohi ta kunshi doka ko gaskiya.

Kotun kolin ta ci gaba da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da yake jawabi ya amince cewa manufar tana da kura-kurai da dama.

Kotun kolin ta bayyana cewa shugaba Buhari ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa ta hanyoyin da ya bayar da umarnin sake fasalin Naira da CBN ya yi.

A hukuncin da aka yanke, kotun ta ce wannan umarnin shugaban kasa ya yi ta ba bisa ka'ida ba, ya jawo wa 'yan kasar tabarbarewar tattalin arziki da ba a taba ganin irinsa ba ta hanyar hana su mallaki da kuma samun kudadensu.

Mai shari’a John Inyang Okoro wanda ya jagoranci kwamitin mutane bakwai na kotun ya sanya ranar 22 ga watan Fabarairu a yau kotun ta bayyana hukuncin da ta yanke kan karar.



Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *