Tinubu Ya Karbi Takardar Shaidar Lashe Zabe daga INEC 

Zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya karbi takardar shaidar lashe zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC..

Rahma ta ruwaito cewa Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya mika wa Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima takardar shaidar a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

Yayin jawabin da ya gabatar a taron, Tinubu ya roki ‘yan Najeriya musamman magoya bayan jam’iyyun adawa da su bashi hadin kai wajen samar da ci gaba ga Najeriya, ba tare da la’akari da banbancin ra’ayi ba.

Sabon zababben shugaban ya kuma ce kofarsa a bude take, ga duk wanda zai kawo shawarar da za ta taimaka wajen fitar da kasar daga cikin kangin da take ciki.

A cikin jawabin nasa, mai cike da sakonni, Bola Ahmed Tinubu yana mai fatan ganin nan gaba an dama da matasa da mata a fannoni daban-daban, wajen gina sabuwar Najeriya, ta yadda za ta yi gogayya da wasu manyan kasashen duniya.

One Reply to “Tinubu Ya Karbi Takardar Shaidar Lashe Zabe daga INEC ”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *