Yau INEC Za Ta Ci Gaba Da Karbar Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Abuja

A safiyar yau Litinin ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa a cibiyar tattara sakamakon zaben na kasa da ke Abuja.

A ranar Lahadi da dare ne dai Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya dage tattara sakamakon bayan karbar na Jihar Ekiti, wanda baturen zaben jihar, Farfesa Ayobami, ya gabatar.

Farfesa Yakubu, ya ce za a ci gaba da aikin da misalin karfe 11 na safiyar Litinin, lokacin da ake fata an kawo sakamakon zaben sauran jihohi 35 da kuma birnin tarayya.

Sakamakon zaben shugaban kasa na Jihar Ekiti ya nuna cewa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC ya samu kuri’a 210,494, Atiku Abubakar na PDP 89,554, Peter Obi na LP 11,397 sai Rabiu Kwankwaso na NNPP kuri’a 264.

A ranar Asabar aka gudanar da zaben shugaban kasa, inda sa’o’i kadan kafin ranar shugaban hukumar ya ba da tabbacin cewa a wannan karon hukumar za ta fitar da sakamakon zabon a kan kari ba kamar yadda aka yi a baya ba.

Idan za a iya tunawa dai, a zaben shugaban kasa na 2019, sai a ranar Talata INEC ta sanar da wanda ya ci, bayan kammala zaben a ranar Asabar.

2 Replies to “Yau INEC Za Ta Ci Gaba Da Karbar Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Abuja”

  1. Alhamdu likkahi mu na kyakkyawan fata ga profs mahmud yakubu Allah ya karfafi gwiwar sa kuma duk wanda Allah ya zaba ma na mu na maraba da zabin uban giji Allah ya sa mu amfana da duk wanda ya samu nasarar hawa wannan kujera ko ya na so ko ba ya so. Hukumar zabe ta kasa ta yi rawar gani an samu canje-canje wadanda su ka yi tasiri wajen gudanar da zabe cikin sauki da hanzari Alhamdu lillahi.

  2. Alhamdu likkahi mu na kyakkyawan fata ga profs mahmud yakubu Allah ya karfafi gwiwar sa kuma duk wanda Allah ya zaba ma na mu na maraba da zabin uban giji Allah ya sa mu amfana da duk wanda ya samu nasarar hawa wannan kujera ko ya na so ko ba ya so. Hukumar zabe ta kasa ta yi rawar gani an samu canje-canje wadanda su ka yi tasiri wajen gudanar da zabe cikin sauki da hanzari Alhamdu lillahi.

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *