Kwankwaso Ya Cinye Karamar Hukumar Ganduje

Dan takarar shugan kasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya samu nasara a karamar hukumar Gwamnan Jihar Kano na APC Abdullahi Umar Ganduje.

Jami’in tattara sakamakon zabe, Adamu Jibril ne ya sanar da cewa Kwankwaso ne ya yi nasara a Karamar Hukumar Dawakin Tofa, mahaifar Ganduje.

Kwankwaso ya samu kuriu 25,072 inda dan takarar APC Bola Tinubu ya samu kuri’u 16,773.

Atiku Abubakar na PDP ya tashi da kuri’u 2,477 sannan Peter Obi na Labor ya samu 202.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *