Shuguna Sun Kone A Gobarar Monday Market, Maiduguri

Ana fargabar gobarar dare ta lakume dubban shaguna a Monday Market, babbar kasuwar da ke cikin birnin Maiduguri, na Jihar Borno.

Wakilanmu da ke a can sun bayyana mana cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe biyu 2 na dare kuma ta lakume kayayyakin da darajarsu ta kai biliyoyin Naira.

Shaidu sun bayyana cewa hatta bankunan da ke cikin kasuwar ma wuta ta ci su, wanda suka tabbatar da ganin biyu na ci da wuta.

Haka nan kuma wakilanmu sun ga matasa na yin awon gaba da kayayyakin da aka ceto daga gobarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *