INEC Ta Soke Zaben Akwati 7 A Kogi

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke zaben wasu akwati guda bakwai a Mazabar Kogi ta Gabas sakamakon tarzomar ’yan daba.

INEC ta ce sokewar ta shafi akwati biyu a yankin Anyigba, da wasu biyar a kauyen Omala da ke jihar ta Kogi.

Ta kara da cewa harin da ’yan daban suka kai inda suka hargitsa rumfunan zabe tare da harba bindiga, ya saba wa Dokar Zabe.

Ta ce harin ya sa tilas aka dakatar da zabe a yankunan da lamarin ya shafa.

INEC ta ce akwati na 01 da ke Gundumar Abejukolo cikin Karamar Hukumar Omala, na daga cikin akwatunan da aka soke zabensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *