INEC: “Mun kammala dukkan shirye shiryen da suka kamata wajen ganin an samu nasarar zaben da zai gudana a wannan shekara ta 2023”.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye shiryen da suka kamata wajen ganin an samu nasarar zaben da zai gudana a wannan shekara ta 2023.

Mai magana da yawun hukumar ta INEC a matakin kasa Hajiya Zainab Aminu Abubakar ce ta bayyana hakan yayin tattaunawa da ita cikin shiri na musamman a tashar Rahma Radio da ke birnin tarayya Abuja.

Hajiya Zainab wadda tayi dogon bayani game da dukkan shirye shiryen da hukumar ta INEC ta kammala zuwa yanzu, tace sun gama aikawa da rukunin farko na kayan zaben da doka ta bayar da dama a aike da su wadanda ake kira da non-sensitive materials, da kuma sanya hannu da kungiyoyin sufurin mota da jiragen ruwa wadanda zasu yi jigilar ma’aikata da kayan aiki ga dukkan mazabu da ke fadin kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *