An shawarci masu yiwa kasa hidima da zasu yi aikin zaben da ke tafe da su bawa tsaron lafiyarsu kulawa ta musamma a yayin gabatar da aikin.

Babban daraktan hukumar masu yiwa kasa hidima ta NYSC, Brig- General Dogara Ahmed ya shawarci masu yiwa kasa hidima da zasu yi aikin zaben da ke tafe da su bawa tsaron lafiyarsu kulawa ta musamma
a yayin gabatar da aikin.

Babban daraktan wanda ya bayyana a haka a yayi da yake zantawa da manema labarai ya kuma yi kira a gare su da kada su yarda yan siyasa suyi amfani da su wajen aikata magudin zabe domin gujewa zubar wa
da hukumar mutunci.

Ya kuma tabbatawar da masu yiwa kasa hidimar cewa hukumar zabe mai zaman kanta tayi alkawarin daukar dukkanin dauwainiyyarsu a yayi gabatar da aikin, tare da bukatar dasu mika dukkanin korafe korafinsu
da zasu iya samu a yayin aikin ga shugabannin hukumar zabe dake
kananan hukumomin da aka tura su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *