Shugaba Vladimir Putin ya sanar da ficewar Rasha a yarjejeniyar makamin nukiliya da ta kulla da Amurka

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da ficewar Rasha a yarjejeniyar makamin nukiliya da ta kulla da Amurka, sannan ya zargi kasashen Yamma da ta’azzara rikicin Ukraine, gabanin wani muhimmin jawabi da shugaban Amurka Joe Biden zai yi.

A jawabinsa ga al’ummar kasar, gabanin bikin cika shekara da fara yaki a Ukraine, Putin ya kuma sha alwashin cewa Rasha za ta ci gaba da yaki a Ukraine tare da cimma manufofinta bisa tsari.

Ya ce Moscow ba za ta sake shiga cikin sabuwar yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya ta START ba amma ba za ta fice daga yarjejeniyar gaba daya ba. Sai dai Rasha ta ce za ta ci gaba da lura da takunkumin da aka sanya kan batun nukiliyar da sabuwar yarjejeniya.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta fitar ta ce: “Rasha na da niyyar bin tsarin da ya dace kuma za ta ci gaba da bin ka’idoji na takaita kera makaman nukiliya’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *