NRC ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasa

Hukumar Sufurin Jirgin Kasa ta Kasa (NRC) ta ba da sanarwar dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasa daga ranar Asabar, 25 zuwa Litinin, 27 ga Fabrairu.

Mai magana da yawun hukumar, Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana haka ga manema labarai ya kuma kara da cewa, an dakatar da zirga- zirgar ne domin baiwa ‘yan Najeriya damar kada kuri’a su a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a gudanar a ranar 25 ga wata Fabrairu.

A cewarsa, jiragen da lamarin ya shafa su ne, na Abuja-Kaduna da Warri-Itakpe da Legas-Ibadan da kuma Lagos-Ijoko.

Yakubu ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen kasa daga ranar Talata 28 ga watan Fabrairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *