A wani saƙo da sarkin malaman Sokoto, kuma sakataren kwamitin ganin watan Malam Yahaya Muhammad Boyi ya aika wa da BBC ya ce mai alfarmar sarkin musulmin ya tsayar da ranar Laraba a matsayin 1 ga watan Sha’aban.
Tun da farko dai kwamitin ganin wata na mai alfarma sarkin Musulmin
ya wallafa a shafinsa Tuwita cewa kasancewar ba su samu labarin ganin jinjirin watan ranar Litinin ba.
Mai Alfarma sarkin musulmin ya sanar da ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu a matsayin ranar 1 ga watan Sha’aban.
Ganin watan na Sha’aban, abu ne mai matuƙar muhimmanci ga al’ummar Musulmi, saboda shi ne watan ƙarshe kafin na Ramadan, wata mai tsarki da suke azumi tsawon kwana 29 ko 30.