INEC: “Dukan ‘yan takarar shugaban ƙasa za su bayyana a ranar Laraba domin sa hannu kan yarjejeniyar amincewa a gudanar da zaɓe lami lafiya”

Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa za su bayyana a ranar Laraba, domin su sa hannu kan yarjejeniyar amincewar yarda a gudanar da zaɓe lami lafiya, ba tare da tashin hankali ba.

Yakubu ya bayyana haka a lokacin ganawar sa da ‘yan jarida, bayan ya kai ziyara Makarantar Sakandire ta Garki, Abuja, inda ake bayar da horo ga Masu Sa-ido Kan Jami’an Zaɓe (SPO).

Shugaban na INEC ya kuma kai irin wannan ziyarar a Cibiyar Taro ta Duniya(ICC), inda ya ce a can ne jihohi za su riƙa aikawa da sakamakon zaɓe ana tattarawa.

Daga ƙarshe kuma a can ne shugaban na INEC zai bayyana ɗan takarar da ya yi nasara, tare da sakamakon da kowane ɗan takara ya samu.

Yakubu ya ce haka kuma ICC zai kasance Cibiyar Yaɗa Labarai.

Haka kuma Yakubu ya ce INEC ba za ta fuskanci matsalar ƙarancin kuɗi ba, bisa dogaro da alƙawarin da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi wa shugaban na INEC, a lokacin da ya ziyarce shi.

Ya ce yawancin ayyukan da INEC za ta biya ma’aikata duk tura masu a asusun ajiyar su za ta yi.

Da ya ke magana kan ƙalubalen tsaro, ya ce wannan aikin jami’an tsaron
ƙasa ne, kuma sun yi alkawarin babu wani gagararren da za’a bari ya haifar
wa zaɓen 2023 da cikas.
Ya ce Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na Ƙasa da ke ƙarƙashin Tsohon
Shugaban Ƙasa, Abdulsalami Abubakar, shi ne zai shirya taron rattaba
hannun amincewar da ‘yan takarar za su yi a ranar Laraba, 22 ga Fabrairu,
2023, a cibiyar ICC a Abuja.
Ya ce INEC ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen 2023 a cikin
kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *