Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake bai wa ‘yan Najeriya hakuri dangane da halin da matsin da suka shiga sakamakon wasu daga cikin manufofin da gwamnatinsa ke aiwatarwa.
Buhari ya yi wannan roko ne cikin wani bidiyo da aka nada daga birnin Addis Ababa, inda yake halartar taron shugabannin kasashen Afirka na kungiyar AU a kasar Habasha.
Wannan dai shi ne karo na biyu cikin kasa da wata guda da shugaban Najeriyar ke neman afuwar ‘yan kasar a dangane da halin matsin da suka shiga na karancin takardun kudin Naira, sakamakon cikar wa’adin daina amfani da tsaffin takardun dubu 1 da 500 da aka sauyawa fasali.
Tuni da shirin sake fasalin nairar ya haifar da cikas ga harkokin kasuwanci a sassan Najeriya, musamman a tsakanin kananan ‘yan kasuwa a yankunan karkara, inda ba a saba dogaro da asusun bankuna ba. Ita kuwa gwamnati ta cigaba da nanata bayanin cewa, ta sauya fasalin takardun nairar na dubu 1 da 500 da kuma 200 ne, tare da takaita yawan wadanda ke hannun jama’a, da kyakkyawar manufar inganta tattalin arziki, yakar masu sama da fadi da kudaden gwamnati da kuma dakile sauran laifuka masu alaka da kudaden.
Sai dai har yanzu wannan al’amari na cigaba da zama muhimmin batun dake ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, musamman bayan da Kotun Kolin kasar ta bayar da umarnin dakatar da shirin daina amfani da tsaffin takardun kudin na Naira, amma kuma gwamnatin Tarayya ta yi biris da umarnin.
Kwana guda bayan hukuncin Kotun ne kuma shugaban Najeriya Muhammmadu Buhari, yayin jawabi ta kafar talabijin ya nanata cewar batun daina amfani da tsaffin takardun dubu 1 da 500 na nan daram, sai dai ya sassauta akan Naira 200, wadda ya bayar da umarnin za a cigaba da amfani da ita har zuwa nan da kwanaki sittin.
Gwamnonin jihohi 11 ne ke kalubbalantar shirin sake fasalin Nairar a gaban Kotun Kolin Najeriya, wadda za ta yanke hukunci akan lamarin a ranar 22 ga wannan wata na Fabarairu, kan karar da gwamnonin shuka shigar.
Sai dai har yanzu wannan al’amari na cigaba da zama muhimmin batun dake
ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, musamman bayan da Kotun Kolin kasar ta
bayar da umarnin dakatar da shirin daina amfani da tsaffin takardun kudin na
Naira, amma kuma gwamnatin Tarayya ta yi biris da umarnin.
Kwana guda bayan hukuncin Kotun ne kuma shugaban Najeriya
Muhammmadu Buhari, yayin jawabi ta kafar talabijin ya nanata cewar batun
daina amfani da tsaffin takardun dubu 1 da 500 na nan daram, sai dai ya
sassauta akan Naira 200, wadda ya bayar da umarnin za a cigaba da amfani
da ita har zuwa nan da kwanaki sittin.
Gwamnonin jihohi 11 ne ke kalubbalantar shirin sake fasalin Nairar a gaban
Kotun Kolin Najeriya, wadda za ta yanke hukunci akan lamarin a ranar