CBN ya jefa ’yan Najeriya cikin rudani bayan ya fitar da sanarwa masu cin karo da juna kan ci gaba a karbar tsoffin takardun

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jefa ’yan Najeriya cikin rudani bayan ya fitar da sanarwa masu cin karo da juna kan ci gaba a karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 cikin dan kankanin lokaci.


CBN ya lashe amansa ne bayan manyan bankunan kasuwanci irinsu UBA da First Bank sun tura wa abokan huldarsu sakonni cewa za su ci gaba da karbar tsoffin takardun N500 da N1,000.

Bankunan sun yi haka ne bayan wata sanarwar da kakakin CBN, Osita Nwanisobi, da ke umartar su da karbar kudin matukar ba su wuce N500,000 ba.

Bayan fitowar wasikar, ’yan jarida sun tuntubi Mista Nwanisobi, game da ita, wanda ya tabbatar musu da sahihancinta.

Amma kafin a jima, bayan kafofin watsa labarai su wallafa labarin, sai CBN ya fitar da wata sabuwar sanarwa, yana karyata umarninsa na farko da ya baiwa bankuna su ci gaba da karbar tsofaffin N500 da N1000.

A sabuwar sanarwar, kakakin na CBN ya zargi kafofin watsa labarai da yada labarin karya — wato sanarwarsa ta farko wadda shi da kansa ya tabbatar musu da sahihancinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *