Buhari ya ja kunnen masu ‘yaɗa jita-jitar’ kafa gwamnatin riƙon kwarya a Najeriya.

Fadar shugaban Najeriya ta ce babu ƙamshin gaskiya cikin kalaman da ake yaɗawa kan cewa Muhammadu Buhari na shirin miƙa mulki ga gwamnatin riƙon ƙwarya.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan lamuran yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya ce, “ya kamata a daina ɗaukar lamarin gwamnatin riƙo da wasa, maganar zaɓe na nan daram.”

Yayin da aka jiyo wasu shugabannin na zargin cewa Shugaba Buhari na neman daƙile kafafun dimokradiyyar Najeriya, a wani gefen kuma iƙirari ne kan cewa ƙarancin naira da ake fama da shi a Najeriya wani ɓangare ne na janyo koma baya ga zaɓe mai zuwa da za a gabatar nan da kwanaki, da kuma
shirin miƙa iko ga gwamnatin riƙo.

A nasa martanin kakakin shugaban ƙasar ya ce wannan wani salo ne mai
cike da haɗari da wasu mutane suka ɗauka waɗanda suke ganin za su iya
faɗuwa zaɓen.
Ya ƙara da cewa ƙirƙiro yanayin da zai jefa mutane cikin firgici ba hanya ba
ce da za ta kawo ƙarshen damuwar da aka shiga ba ta sauyin naira.
Yace sauyin kuɗin ba a ƙirƙiro shi ba ne domin ya bai wa shugaban ƙasa
damar zama a kan karagar mulki har bayan 29 ga watan Mayu, yana cewa
“fadar shugaban ƙasa a shirye take ta miƙa mulki ga duk wanda ya ci zaɓe
domin gadar Shugaba Buhari.
Kuma za a yi hakan ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023 kamar yadda kundin
tsarin mulki ya tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *