An samu ɓarkewar yamutsi a wajen ofishin CBN da ke Legas

An samu ɓarkewar yamutsi a wajan ofishin babban bankin Najeriya da ke birnin Lagos sakamakon ƙarancin kuɗin da ake fuskanta a ƙasar.

Ɗaruruwan mutane waɗanda suke son su musanya tsofaffin takardun kuɗinsu da sabbin sun yi wa bankin ƙawanya.

Wasu sun yi ƙoƙarin haura wa ta katangar da ta kewaye ginin. Sai dai babban bankin ya fitar da wata sanarwa in da ya musanta cewa ya bayar umurci bankunan kasuwancin suka ci gaba da karɓar tsoffafin
takardun kuɗin naira 500 da 100.

Ƙarancin takardun kuɗin ya janyo ɓarkewar tarzoma a wasu sassan Najeriya a baya bayan nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *