Hukumar Kula da aikin Hajji ta Kasa NAHCON, ta bukaci hukumomin jindadin alhazan Jihohi da su biya kashi 40 cikin dari na kudin kujerun aikin hajjin wannan shekara ta 2023 da aka basu kafin ranar 28 ga wannan wata na Febrairun 2023.
Hakan na kunshe cikin sanarwar da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Musa Uban Dawaki ya sanayawa hannu inda ya ce yin kan zai bawa hukumar damar cigaba da shirye-shiryen aikin hajjin akan lokaci, musanman su biya kudade ga hukumomin Kasar Saudia Arebiya da zasu yiwa alhazan Najeriya hidama a yayin aikin Hajjin .
Sanarwar tace hukumar ta gano cewar wasu hukumomin jin dadin alhazai na jihohin na kawo nakasu ga tsarin sanaya kudin ajiya a asusun adashin gata da maniyyata ke ajiya , suke karbarkudin kaitsaye daga maniyyatan domin yi musu rijisra.
NAHCON ta jadda cewar a karkashin shirin aikin hajji na shekarar 2023 hukumar ta ware kashi Arba’in cikin dari na kujerun jihohi ga maniyyatan da suka sanya kudaden ajiyar su a asusun adashin gata tare da ware kaso 60 ga wadanda suka biya kai tsaye a hukumomin jin dadin alhazai na jihohinsu inda ta bukaci sakatarorin hukumomin jindadin alhazan da su mutunta yarjejeniyar.
Akarshe hukumar aikin hajjin ta kasa ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkokin aikin hajjin da su cigaba da bada goyan bayansu ga hukumar domin gudanar da aikin hajjin na bana cikin nasara.