Bashir Ahmad Ga Ganduje: “Ka Kai Kudinka CBN Idan Na Halal Ne”.

Mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya bukaci gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, kan cewar idan ya tabbatar kudinsa na halal ne ya kai su CBN. 

Ahmad ya mayar wa Ganduje martani ne kan sukar da ya yi wa Buhari, biyo bayan umarnin Shugaban Kasar na ci gaba da amfani da tsohuwar takardar Naira 200.

Ganduje ya zargi Buhari da bullo da wannan tsari na sauya fasalin kudi don kayar da jam’iyyar APC a zaben da ke tafe.

Sai dai kuma a martanin da hadimin Shugaban Kasar ya mayar wa Ganduje, ya ce idan gwamnan ya isa ya kai kudadensa ga Babban Bankin Najeriya matukar ta hanyar halal ya same su.

A cewarsa, da yawa daga cikin gwamnonin jihohin da suka ki amincewa da tsarin, suna tayar da jijiyoyin wuya ne don bukatar kansu ba ta talakawa.

“Mutane da yawa sun dauka wadanda ke fafutuka a kan wannan tsari suna yi don talakawa, ba su san don kan su suke yi ba.

“Sun boye makudan kudade suna tsoron kai wa CBN saboda gudun haduwa da EFCC da NFIU.

Kazalika, cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, hadimin Shugaban Kasar ya magana mai harshen damo, inda ya ce: “Baba Dan Audu, Shugaba Baba Buhari ya bayar da umarnin ku kai kudinku CBN. Idan EFCC da NFIU suka tabbatar da na halal ne za ka samu sakon kudinka.”

Bashir Ahmad ya kuma musanta zargin da Ganduje ya yi wa Buhari na cewar yana kokarin lalata dimokuradiyya.

“Ban tabbatar da cewa dimokuradiyya ta lalace ba, sai ranar zaben fid-da-gwanin da na yi takara, kiri-kiri aka aiko daga sama aka yi mana murdiya a bainar jama’a, wai kawai saboda mu ‘yan siyasar Abuja ne.”

Ana iya tuna cewa, Bashir Ahmad dai ya nemi tsayawa takarar dan Majalisar Tarayya mai wakilatar kananan hukumomin Gaya, Takai da Sumaila, sai dai bai yi nasara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *